3 Lokacin da kake yaƙi dominmu, al'ummai sukan gudu daga bakin dāga.
4 Akan tsirga a bisa abubuwan da suke da su, a kwashe su ganima.
5 Ubangiji da girma yake! Yana mulki a kan kome. Zai cika Urushalima da adalci da mutunci,
6 zai kuma sa aminci cikin al'ummar. A koyaushe yakan kiyaye jama'arsa ya kuma ba su hikima da sani. Dukiyarsu mafi girma ita ce tsoron Ubangiji.
7 Mutane masu jaruntaka suna kira don a taimake su! Jakadu waɗanda suke ƙoƙarin kawo salama suna kuka mai zafi.
8 Manyan karauku suna da hatsari har ba mai iya binsu. Aka keta yarjejeniya, aka ta da sharuɗa. Ba a kuma ganin girman kowa.
9 Ƙasar na zaman banza, an gudu an bar ta. Jejin Lebanon ya bushe, kwarin Sharon mai dausayi ya zama kamar hamada, a Bashan kuma da a kan Dutsen Karmel sai ganyaye suke karkaɗewa daga itatuwa.