2 Ba zai yi tsawa ko ya ta da muryarsa ba,Ko ya yi jawabi da babbar murya a tituna.
3 Zai lallaɓi marasa ƙarfi,Ya nuna alheri ga tafkakku.Zai kawo madawwamiyar gaskiya ga duka.
4 Ba zai fid da zuciya ko ya karai ba,Zai kuma kafa gaskiya a duniya,Manisantan ƙasashe sun zaƙu, suna jiran koyarwarsa.”
5 Allah ya halicci sammai ya kuma shimfiɗa su,Ya yi duniya, da dukan masu rai nata,Ya ba da rai da numfashi ga dukan mutanenta.Yanzu kuwa Ubangiji Allah ya ce wa bawansa,
6 “Ni Ubangiji, na kira ka, na kuma ba ka ikoDomin ka ga ana aikata gaskiya a duniya.Ta wurinka zan yi wa dukan mutane alkawari,Ta wurinka zan kawo haske ga al'ummai.
7 Za ka buɗe idanun makafi,Ka kuma kwance waɗanda suke ɗaure a kurkuku masu duhu.
8 “Ni kaɗai ne Ubangiji Allahnka.Ba wani allahn da zai sami ɗaukakata,Ba zan bar gumaka su sami yabona ba.