1 Sairus shi ne zaɓaɓɓen sarki na Ubangiji!Ubangiji ya sa shi ya ci al'ummai,Ya aike shi ya tuɓe ikon sarakuna,Ubangiji zai buɗe masa ƙofofin birni.Ubangiji ya ce wa Sairus,
2 “Ni kaina zan shirya hanya dominka,Ina baji duwatsu da tuddai.Zan kakkarye ƙyamaren tagulla,In kuma daddatse gagara badau na baƙin ƙarfe.
3 Zan ba ka dukiya daga cikin duhu, a asirtattun wurare,Sa'an nan za ka sani ni ne Ubangiji,Allah na Isra'ila kuma, shi ne ya zaɓe ka.
4 Na sa ka domin ka taimaki bawana Isra'ila,Jama'ar da ni na zaɓa.Na ba ka girma mai yawa,Ko da yake kai ba ka san ni ba.