5 Ubangiji ya ce wa Babila,“Ki zauna shiru a cikin duhu,Ba za su ƙara kiranki sarauniyar al'ummai ba!
6 Na yi fushi da mutanena,Na maishe su kamar su ba nawa ba ne.Na sa su a ƙarƙashin ikonki,Ba ki kuwa yi musu jinƙai ba,Har da tsofaffi ma kin ba su wuya.
7 Kina tsammani za ki yi ta zama sarauniya kullayaumin,Ba ki ɗauki waɗannan al'amura a zuci ba,Ko ki yi tunanin yadda za su ƙare.
8 “Ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi,Ke da kike tsammani kina zaune lami lafiya.Kin ɗauka kina da girma kamar Allah,Har kina ganin ba wani kamarki.Kina tsammani ba za ki taɓa zama gwauruwa ba,Ko ki sha hasarar 'ya'yanki.
9 Amma ba da jimawa ba, a rana ɗayaDukan waɗannan al'amura za su faru.Kome sihirin da za ki yi,Za ki rasa 'ya'yanki, ki kuwa zama gwauruwa.
10 “Kin amince da kanki cikin muguntarki,Kina tsammani ba wanda yake ganinki.Hikimarki da saninki suka sa kika ɓata,Kika kuwa ce da kanki, ‘Ni ce Allah,Ba mai kama da ni!’
11 Duk da haka bala'i zai auko miki,Ba ɗaya daga cikin sihirinki da zai tsai da shi ba,Lalacewa za ta auko a kanki farat ɗaya,Lalacewar da ba ki taɓa ko mafarkinta ba!