13 Don haka za a kwashe ku, ku zama 'yan sarƙa, a raba ku da ƙasarku. Yunwa za ta kashe shugabanninku, sauran jama'a kuwa ƙishirwa za ta kashe su.
14 Lahira ta ƙosa, ta wage bakinta. Ta lanƙwame manyan mutanen Urushalima da sauran babban taron jama'a masu hayaniya.
15 Za a kunyatar da kowa, dukan masu girmankai za a ƙasƙantar da su.
16 Amma Ubangiji Mai Runduna yana nuna girmansa ta wurin aikata abin da yake daidai, yana kuma bayyana shi Mai Tsarki ne, ta yadda yake shara'anta jama'arsa.
17 A cikin kangwayen birnin, raguna za su ci ciyawa, a nan ne kuma awaki za su sami wurin kiwo.
18 Kun shiga uku! Ba ku iya kuɓuta daga zunubanku ba.
19 Kukan ce, “Bari Ubangiji ya gaggauta ya aikata abin da ya ce zai yi don mu gani. Bari Allah, Mai Tsarki na Isra'ila, ya i da shirye-shiryensa. Bari mu ga abin da yake nufi.”