1 Wane ne zai gaskata abin da muka ji yanzu?Wane ne zai iya ganin ikon Ubangiji cikin wannan?
2 Nufin Ubangiji ne bawansa ya yi girmaKamar dashe wanda yake kafa saiwarsa a ƙeƙasasshiyar ƙasa.Ba shi da wani maƙami ko kyan ganinDa zai sa mu kula da shi.Ba wani abin da zai sa mu so shi,Ba kuwa abin da zai ja mu zuwa gare shi.
3 Muka raina shi, muka ƙi shi,Ya daure da wahala da raɗaɗi.Ba wanda ya ko dube shi.Muka yi banza da shi kamar shi ba kome ba ne.
4 Amma ya daure da wahala wadda a ainihi tamu ce,Raɗaɗin da ya kamata mu ne za mu sha shi.Mu kuwa muna tsammani wahalarsaHukunci ne Allah yake yi masa.
5 Amma aka yi masa rauni saboda zunubanmu,Aka daddoke shi saboda muguntar da muka aikata.Hukuncin da ya sha ya 'yantar da mu,Dūkan da aka yi ta yi masa, ya sa muka warke.
6 Dukanmu muna kama da tumakin da suka ɓata,Ko wannenmu ya kama hanyarsa.Sai Ubangiji ya sa hukunci ya auko a kansa,Hukuncin da ya wajaba a kanmu.
7 Aka ƙware shi ba tausayi,Amma ya karɓa da tawali'u,Bai ko ce uffan ba.Kamar ɗan rago wanda ake shirin yankawa,Kamar tunkiya wadda ake shirin yi wa sausaya,Bai ko ce uffan ba.