16 to, zan hukunta ku. Zan aukar muku da bala'i, da cuce-cuce da ba su warkuwa, da zazzaɓin da zai lalatar muku da ido, rai zai zama muku da wahala. Za ku yi shuka a banza gama maƙiyanku ne za su ci.
17 Zan yi gāba da ku in sa maƙiyanku su ɗibge ku, waɗanda suke ƙinku za su mallake ku. Za ku yi ta gudu ba mai korarku.
18 “Amma idan duk da haka ba ku kasa kunne gare ni ba, sai in tsananta hukuncinku har sau bakwai saboda zunubanku.
19 Zan karya ikonku wanda kuke fariya da shi, in hana ruwan sama, ƙasa kuma ta zama kamar tagulla.
20 Za ku ɓarnatar da ƙarfinku a banza gama ƙasarku ba za ta ba da amfaninta ba, itatuwan ƙasar kuma ba za su ba da 'ya'ya ba.
21 “Idan har yanzu kuka tayar mini, ba ku kasa kunne gare ni ba, sai in ƙara yawan hukuncinku har sau bakwai, saboda zunubanku.
22 Zan kuwa turo muku mugayen namomin jeji waɗanda za su kashe 'ya'yanku, su hallakar da dabbobinku, su sa ku zama kaɗan, har ba mai gilmayya a hanyoyinku.