16 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tattaro mini mutum saba'in daga cikin dattawan Isra'ila waɗanda aka sani su ne dattawa da shugabannin jama'ar, ka kawo su a alfarwa ta sujada, ka sa su tsaya tare da kai.
17 Ni kuwa zan sauko, in yi magana da kai a can. Zan ɗiba daga cikin ruhun da yake cikinka, in ba su. Su kuma za su ɗauki nawayar jama'ar tare da kai, domin kada ka ɗauki nawayar kai kaɗai.
18 Ka ce wa jama'ar, su tsarkake kansu don gobe, za su ci nama, gama Ubangiji ya ji gunagunin da suka yi, da suka ce, ‘Wa zai ba mu nama mu ci? Ai, zama cikin Masar ya fi mana.’ Domin haka Ubangiji zai ba su nama, za su kuwa ci.
19 Ba ma don kwana ɗaya, ko biyu, ko biyar, ko goma, ko ashirin kaɗai za su ci ba.
20 Amma har wata guda cur. Za su ci har ya gundure su, ya zama musu abin ƙyama saboda sun ƙi Ubangiji wanda yake tare da su, suka yi gunaguni a gabansa , suna cewa, ‘Me ya sa ma, muka fito Masar?’ ”
21 Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Mutum dubu ɗari shida (600,000) ne suke tafe tare da ni, ga shi kuwa, ka ce za ka ba su nama, za su ci har wata guda cur.
22 Za a yanyanka musu garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu, don su ishe su? Ko kuwa za a tattara musu dukan kifayen teku don su ishe su?”