12 Na roƙe ka kada ka bari ta zama kamar matacce wanda rabin jikinsa ruɓaɓɓe ne a lokacin da aka haife shi.”
13 Sai Musa ya roƙi Ubangiji, ya ce, “Ina roƙonka, ya Allah, ka warkar da ita.”
14 Amma ubangiji ya ce wa Musa, “Da a ce mahaifinta ne ya tofa mata yau a fuskarta, ba za ta ji kunya har kwana bakwai ba? Bari a fitar da ita a bayan zangon kwana bakwai, bayan haka a shigar da ita.”
15 Aka fitar da Maryamu a bayan zangon har kwana bakwai. Jama'ar kuwa ba su ci gaba da tafiya ba, sai da aka shigar da Maryamu a zangon.
16 Bayan wannan jama'a suka tashi daga Hazerot suka sauka a jejin Faran.