5 Sa'an nan ya ce wa Kora da ƙungiyarsa, “Da safe Ubangiji zai nuna mana wanda yake nasa, zai sa wanda yake nasa, wato wanda ya zaɓa, ya sadu da shi a bagade.
6 Kai, Kora da ƙungiyarka duka, gobe, sai ku ɗauki farantan ƙona turare.
7 Ku zuba wuta a ciki, ku kuma zuba musu turaren wuta a gaban Ubangiji. Sa'an nan ne za mu ga wanda Ubangiji ya zaɓa tsakaninmu. Ku Lawiyawa ku ne kuka fi fiffiƙewa!”
8 Musa ya ci gaba da magana da Kora. “Ku Lawiyawa ku kasa kunne!
9 Kuna ganin wannan ƙaramar magana ce, wato cewa Allah na Isra'ila ya keɓe ku daga cikin jama'ar Isra'ila domin ya kawo ku kusa da shi, ku yi aiki a alfarwar sujada ta Ubangiji, ku kuma tsaya a gaban jama'a don ku yi musu aiki?
10 Ya yarda ka zo kusa da shi, kai da dukan 'yan'uwanka Lawiyawa, a yanzu kuwa sai ƙoƙari kuke ku karɓi aikin firist!
11 Kai da ƙungiyarka kun haɗa kai kuna yi wa Haruna gunaguni, amma wane ne Haruna? A zahiri tawaye ne kuke wa Ubangiji!”