5 Ku lura da ayyukan Wuri Mai Tsarki da na bagade don kada hasala ta sāke fāɗa wa Isra'ilawa.
6 Ga shi, ni na ɗauki 'yan'uwanku, Lawiyawa, daga cikin mutanen Isra'ila. Kyauta suke a gare ku, waɗanda aka bayar ga Ubangiji don su lura da alfarwa ta sujada.
7 Da kai, da 'ya'yanka za ku yi aikin firist da duk abin da ya shafi bagade da aiki na bayan labule. Ku ne za ku yi wannan aiki. Na ba ku aikin firist ya zama naku. Duk wani dabam wanda ya zo kuwa, za a kashe shi.”
8 Ubangiji ya kuma ce wa Haruna, “Na ba ka aikin lura da hadayuna na ɗagawa, wato sadakokin Isra'ilawa, na ba ka su su zama rabonka da na 'ya'yanka har abada.
9 Abin da ya ragu daga cikin hadaya mafi tsarki da ake miƙa mini zai zama rabonka da na 'ya'yanka, wato daga kowace hadaya, da hadaya ta gari, da hadaya don zunubi, da hadaya don laifi.
10 A wuri mai tsarki za ku ci shi, kowane namiji ya iya ci. Abu mai tsarki ne a gare ka.
11 “Har yanzu kuma duk sadakokin da Isra'ilawa suke bayarwa don hadaya ta ɗagawa da ta kaɗawa, na ba ka, kai da 'ya'yanka mata da maza, a kowane lokaci. Duk wanda yake da tsarki a gidanka zai iya ci.