13 Da safe Bal'amu ya tashi, ya ce wa dattawan Balak, “Ku koma ƙasarku, gama Ubangiji bai yarda mini in tafi tare da ku ba.”
14 Domin haka dattawan Mowab suka tashi, suka koma wurin Balak, suka ce masa, “Bal'amu bai yarda ya biyo mu ba.”
15 Sai Balak ya sāke aiken dattawa da yawa masu daraja fiye da na dā.
16 Suka je wurin Bal'amu, suka ce masa, “Ga abin da Balak ɗan Ziffor ya ce, ‘Kada ka bar wani abu ya hana ka zuwa wurina,
17 gama zan ɗaukaka ka ƙwarai, kome kuwa ka faɗa mini in yi, zan yi, ka zo ka la'anta mini wannan jama'a.’ ”
18 Amma Bal'amu ya amsa ya ce wa barorin Balak, “Ko da a ce Balak zai ba ni gidansa cike da azurfa da zinariya, ba zan yi wani abu ko kaɗan saɓanin umarnin Ubangiji Allahna ba.
19 Amma ina roƙonku ku kwana a nan yau har in san abin da Ubangiji zai faɗa mini.”