21 Da safe sai Bal'amu ya tashi ya yi wa jakarsa shimfiɗa, ya tafi tare da dattawan Mowab.
22 Allah kuwa ya husata don ya tafi, mala'ikan Ubangiji ya tsaya a hanya ya tarye shi. Shi kuwa yana tafe a bisa jakarsa tare da barorinsa biyu.
23 Da jakar ta ga mala'ikan Ubangiji yana tsaye kan hanya da takobi zare a hannunsa, sai ta kauce daga hanya, ta shiga saura. Bal'amu kuwa ya buge ta don ya komar da ita a hanyar.
24 Sai mala'ikan Ubangiji ya je, ya tsaya a inda hanyar ta yi matsatsi a tsakanin bangayen gonakin inabi.
25 Sa'ad da jakar ta ga mala'ikan Ubangiji, ta matsa a jikin bango, ta goge ƙafar Bal'amu ga bangon, sai ya sāke bugunta.
26 Mala'ikan Ubangiji kuma ya sha kanta, ya tsaya a ƙunƙuntaccen wuri inda ba wurin juyawa zuwa dama ko hagu.
27 Da jakar ta ga mala'ikan Ubangiji, sai ta kwanta a ƙafafun Bal'amu. Sai Bal'amu ya husata, ya bugi jakar da sandansa.