14 “Idan baƙo yana zaune a wurinku, shi ma sai ya kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji bisa ga umarnai da ka'idodi na Idin Ƙetarewa. Ka'ida ɗaya ce ga baƙo da ɗan gari.”
15-16 A ranar da aka kafa alfarwa ta sujada, sai girgije ya sauko ya rufe ta. Da maraice kuwa girgijen yana kamar wuta.
17 A duk lokacin da aka gusar da girgijen, sai Isra'ilawa su kama hanya. A inda girgijen ya tsaya, nan kuma Isra'ilawa za su kafa zango.
18 Da umarnin Ubangiji Isra'ilawa suke tashi, da umarninsa kuma suke sauka. Muddin girgijen yana bisa alfarwar, sukan yi ta zamansu a zangon.
19 Ko da girgije ya daɗe a bisa alfarwar Isra'ilawa ba sukan tashi ba, sukan bi umarnin Ubangiji.
20 Wani lokaci girgijen yakan yi 'yan kwanaki ne kawai bisa alfarwar. Tashinsu da zamansu sun danganta ga umarnin Ubangiji.
21 Wani lokaci girgijen yakan zauna a bisa alfarwar daga maraice zuwa safiya ne kawai, sa'an nan ya tashi, su kuma sai su tashi. Amma idan girgijen ya yini, ya kwana, sa'an nan ya tashi, su kuma sai su tashi.