6 Filistiyawa kuwa suka ce, “Wane ne ya yi mana wannan abu?”Sai aka ce, “Samson ne, surukin mutumin Timna, domin ya ɗauki matar Samson ya ba wanda ya yi masa abokin ango.” Filistiyawa kuwa suka je suka ƙone matar, ta mutu, suka kuma ƙone gidan mahaifinta.
7 Samson ya ce musu, “Wato haka kuka yi! To, na rantse, ba zan bari ba sai na rama!”
8 Ya kuwa fāɗa musu, ya kashe su da yawa. Sa'an nan ya tafi ya zauna a kogon dutsen Itam.
9 Filistiyawa suka haura, suka kafa sansani a Yahudiya, suka bazu a cikin Lihai.
10 Mutanen Yahuza suka ce, “Me ya sa kuka kawo mana yaƙi?”Filistiyawa suka ce, “Mun zo ne domin mu kama Samson, mu yi masa kamar yadda ya yi mana.”
11 Sa'an nan mutum dubu uku na Yahuza suka gangara zuwa kogon dutsen Itam. Suka ce wa Samson, “Ba ka sani ba Filistiyawa ne suke mulkinmu? Me ya sa ka yi mana haka?”Shi kuwa ya amsa musu, ya ce, “Kamar yadda suka yi mini, haka ni kuma na yi musu.”
12 Suka ce masa, “Mun gangara zuwa wurinka don mu ɗaure ka, mu miƙa ka gare su.”Samson ya ce musu, “Ku rantse mini idan ba ku ne da kanku kuke so ku kashe ni ba.”