11 Za ka ji abin da suke cewa. Bayan haka za ka sami ƙarfin hali da za ka tafi ka fāda wa sansaninsu.” Gidiyon kuwa ya tafi tare da Fura baransa a gefen sansanin abokan gāba.
12 Madayanawa, da Amalekawa, da mutanen gabas duka suna nan da yawa a shimfiɗe cikin kwarin, kamar fara. Raƙumansu kuma suna da yawa kamar yashi a bakin teku. Ba wanda zai iya ƙidaya su.
13 Sa'ad da Gidiyon ya tafi, sai ya ji wani yana faɗa wa abokinsa mafarkin da ya yi. Ya ce, “Na yi mafarki, na ga wainar sha'ir ta faɗo a tsakiyar sansaninmu. Ta zo ta bugi alfarwa. Alfarwar kuwa ta fāɗi rigingine.”
14 Abokinsa ya amsa, ya ce, “Ai, ba wani abu ba ne. Wannan takobin Gidiyon ne, ɗan Yowash. Ba'isra'ile! Allah ya ba shi nasara kan Madayanawa da dukan rundunanmu!”
15 Da Gidiyon ya ji mafarkin, har da fassarar, sai ya yi sujada, ya koma a sansaninsu na Isra'ilawa. Da ya isa, sai ya ce, “Ku tashi, gama Ubangiji ya ba da rundunar Madayanawa a gare ku.”
16 Sai ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho, da tulu, da jiniya a cikin tulun.
17 Sa'an nan ya ce musu, “Sa'ad da muka kai sansani, sai ku dube ni, ku yi duk abin da nake yi. Yadda na yi, ku ma ku yi haka.