12 Tare da 'yan'uwansu waɗanda suka yi aiki a Haikali, su ɗari takwas da ashirin da biyu ne.Akwai kuma Adaya ɗan Yeroham, jīkan Felaliya. Sauran kakanninsa su ne Amzi, da Zakariya, da Fashur, da Malkiya.
13 Tare da 'yan'uwansu shugabannin gidajen kakanni, su ɗari da arba'in da biyu. Sai kuma Amashai ɗan Azarel, jīkan Azai. Sauran kakanninsa su ne Meshillemot, da Immer.
14 Tare da 'yan'uwansu, su ɗari da ashirin da takwas ne gwarzayen sojoji ne. Shugabansu shi ne Zabdiyel ɗan Haggedolim.
15 Na wajen Lawiyawa kuwa su ne Shemaiya ɗan Hasshub, jīkan Azrikam. Sauran kakanninsa su ne Hashabiya, da Bunni,
16 da Shabbetai, da Yozabad, ɗaya daga cikin manyan shugabanni na Lawiyawa, waɗanda suke lura da kewayen Haikalin Allah.
17 Da kuma Mattaniya ɗan Mika, jīkan Zikri, zuriyar Asaf, shi ne shugaba na farko na mawaƙan addu'a ta godiya. Bakbukiya, shi ne mataimakin Mattaniya. Ga kuma Obadiya ɗan Shemaiya, jīkan zuriyar Galal, zuriyar Yedutun.
18 Dukan Lawiyawa da suke a tsattsarkan birni su ɗari biyu da tamanin da huɗu ne.