3 Tobiya Ba'ammone yana kusa da shi, ya ce, “Ai, garun da suke ginawa da duwatsu, ko dila ya hau, sai ya rushe shi!”
4 Sai ni, Nehemiya, na yi addu'a, na ce, “Ka ji, ya Allahnmu, gama ana raina mu, ka sa ba'arsu ta koma kansu, ka sa a washe su a kai su ƙasar bauta.
5 Kada ka shafe laifinsu, kada kuwa ka gafarta musu, gama sun ci mutuncinmu, mu da muke gini.”
6 Muka gina garun, har ya kai rabin tsayinta, domin mutane sun himmatu da aikin.
7 Amma sa'ad da Sanballat, da Tobiya, da Larabawa, da Ammonawa, da mutanen Ashdod, suka ji yadda ginin garun Urushalima yake ci gaba, ana kuma tattoshe tsattsaguwa, sai suka husata.
8 Dukansu suka ƙulla za su zo, su yi yaƙi da Urushalima, su ta da hankali a cikinta.
9 Sai muka yi addu'a ga Allahnmu, muka sa masu tsaro su yi mana tsaro dare da rana saboda su.