45 Masu tsaron Haikali su ne zuriyar Shallum, da Ater, da Talmon, da Akkub, da Hatita, da Shobai, ɗari da talatin da takwas.
46-56 Ma'aikatan Haikali da suka komo daga zaman talala, su neZuriyar Ziha, da Hasufa, da Tabbawot,Keros, da Siyaha, da Fadon,Lebana, da Hagaba, da Shamlai,Hanan, da Giddel, da Gahar,Rewaiya, da Rezin, da Nekoda,Gazam, da Uzza, da Faseya,Besai, da Me'uniyawa, da Nefushiyawa,Bakbuk, da Hakufa, da Harkur,Bazlut, da Mehida, da Harsha,Barkos, da Sisera, da Tema,Neziya, da Hatifa.
57-59 Iyalan barorin Sulemanu da suka komo daga zaman talala, su nena Sotai, da Hassoferet, da Feruda,Yawala, da Darkon, da Giddel,Shefatiya, da Hattil, da Fokeret-hazzebayim, da Ami.
60 Jimillar zuriyar ma'aikatan Haikali da na Sulemanu, su ɗari uku da tasa'in da biyu ne.
61-62 Waɗannan su ne daga zuriyar Delaiya, da Tobiya, da Nekoda, waɗanda suka zo daga garuruwan Telmela, da Tel-harsha, da Kerub, da Addan, da Immer, amma ba su iya nuna gidajen kakanninsu, ko zuriyarsu a cikin Isra'ilawa ba, su ɗari shida ne da arba'in da biyu.
63 Na wajen firistoci kuma su ne zuriyar Habaya, da na Hakkoz, da na Barzillai, wanda ya auri 'yar Barzillai mutumin Gileyad, aka kira shi da sunan zuriyar surukinsa.
64 Waɗannan suka nema a rubuta su tare da waɗanda aka rubuta jerin sunayen asalinsu, amma ba a same su a ciki ba, saboda haka aka hana su shiga cikin firistoci, sun zama kamar marasa tsarki.