1 Dukan jama'a suka taru wuri ɗaya a filin Ƙofar Ruwa, suka faɗa wa Ezra, magatakarda, ya kawo Attaura ta Musa wanda Ubangiji ya ba Isra'ilawa.
2 A ran ɗaya ga watan bakwai, sai Ezra, firist, ya kawo Attaura a gaban taron jama'a, mata da maza, da dukan waɗanda za su ji, su fahimta.
3 Ya karanta Littafin, yana fuskantar filin Ƙofar Ruwa, a gaban mata da maza, da waɗanda za su iya fahimta. Mutane duka kuwa suka kasa kunne ga karatun Attaura, tun da sassafe har zuwa rana tsaka.
4 Sai Ezra, magatakarda, ya tsaya a wani dakali na itace, wanda suka shirya musamman domin wannan hidima. Sai Mattitiya, da Shema, da Anaya, da Uriya, da Hilkaya, da Ma'aseya, suka tsaya a wajen damansa, a wajen hagunsa kuwa Fedaiya, da Mishayel, da Malkiya, da Hashum, da Hashbaddana, da Zakariya, da Meshullam suka tsaya.
5 Ezra kuwa ya buɗe Littafin a gaban jama'a duka, domin yana sama da jama'a. Sa'ad da ya buɗe Littafin, sai jama'a duka suka miƙe tsaye.