33 Ka yi daidai da ka hukunta mu haka!Kai mai aminci ne, mu kuwa mun yi zunubi.
34 Gama kakanninmu, da sarakunanmu,Da shugabanninmu, da firistocinmu,Ba su kiyaye dokarka ba.Ba su kasakunne ga umarnanka da gargaɗinka ba.Da waɗannan ne kake zarginsu.
35 Da albarkacinka sarakuna suke mulkin jama'arka,Sa'ad da suke ƙasashen waje, ƙasa mai dausayi ka ba su,Amma ba su juyo su bar zunubi, su bauta maka ba.
36 Ga shi, a yau mu bayi ne a ƙasar da ka ba mu,Wannan ƙasa mai dausayi wadda take ba mu abinci.
37 Amfanin ƙasa duk yana tafiya ga sarakunanDa ka ɗora su a kanmu saboda mun yi zunubi.Suna yi mana yadda suka ga dama, mu da dabbobinmu,Muna cikin baƙin ciki.”
38 “Saboda wannan duka muke yin alkawari mai ƙarfi a rubuce. Shugabanninmu kuwa, da Lawiyawanmu, da firistocinmu, suka buga hatimi, suka sa hannu.”