4 Yahaya Maibaftisma ya bayyana a jeji, yana wa'azi mutane su tuba a yi musu baftisma domin a gafarta musu zunubansu.
5 Sai duk mutanen ƙasar Yahudiya, da dukan mutanen Urushalima suka yi ta zuwa wurinsa, suna bayyana zunabansu, yana yi musu baftisma a Kogin Urdun.
6 Yahaya kuwa na sanye da tufar gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma.
7 Ya yi wa'azi ya ce, “Wani na zuwa bayana wanda ya fi ni girma, wanda ko maɓallin takalminsa ma ban isa in sunkuya in ɓalle ba.
8 Ni da ruwa na yi muku baftisma, amma shi da Ruhu Mai Tsarki zai yi muku.”
9 Sai ya zamana a wannan lokaci Yesu ya zo daga Nazarat ta ƙasar Galili. Yahaya ya yi masa baftisma a Kogin Urdun.
10 Da fitowarsa daga ruwan sai ya ga sama ta dāre, Ruhu yana sauko masa kamar kurciya.