10 Sai suka ta da murya da ƙarfi suka ce, “Ya Ubangiji Mamallaki, Mai Tsarki, Mai Gaskiya, sai yaushe ne za ka yi hukunci, ka ɗaukar mana fansar jininmu a gun mazaunan duniya?”
11 Sai aka ba kowannensu farar riga, aka ce musu, su dai huta kaɗan, har a cika adadin abokan bautarsu, wato, 'yan'uwansu, waɗanda za a kashe, kamar yadda su ma aka kashe su.
12 Da ya ɓamɓare hatimi na shida, na duba, sai kuwa aka yi wata babbar rawar ƙasa, rana ta koma baƙa kamar gwado na gashi, gudan wata ya zama kamar jini,
13 taurari kuma suka faɗa a ƙasa kamar yadda ɓaure yake zubar da ɗanyun 'ya'yansa, in ƙasaitacciyar iska ta kaɗa shi,
14 sararin sama ya dāre ya naɗe kamar tabarma, sai aka kawar da kowane dutse, da kowane tsibiri daga mazauninsa.
15 Sai sarakunan duniya, da manyan mutane, da sarakunan yaƙi, da ma'arzuta, da ƙarfafa, da kuma kowane bawa da ɗa, suka ɓuya a kogwanni, da kuma a cikin duwatsu,
16 suna ce wa duwatsun, “Ku faɗo a kanmu, ku ɓoye mu daga idon wanda yake a zaune a kan kursiyin, da kuma fushin Ɗan Ragon nan,