16 Kada ka zaci ni 'yar iska ce. Ni dai ina faɗar damuwata da tsokanar da ake yi mini ne.”
17 Sai Eli ya ce mata, “Ki sauka lafiya, Allah na Isra'ila ya amsa miki roƙonki.”
18 Ita kuma ta amsa, ta ce, “Bari baiwarka ta sami tagomashi a gare ka.” Sa'an nan ta tafi, ta ci abinci. Ba ta ƙara ɓata ranta ba.
19 Elkana da iyalinsa suka tashi tun da sassafe suka yi wa Ubangiji sujada, sa'an nan suka koma gidansu a Rama. Elkana fa ya kwana da matarsa, Hannatu. Ubangiji kuwa ya tuna da ita.
20 Ta yi juna biyu, ta haifa ɗa, ta raɗa masa suna Sama'ila, wato “Na roƙo shi daga wurin Ubangiji.”
21 Elkana da iyalinsa duka suka tafi Shilo domin su miƙa wa Ubangiji hadaya ta shekara shekara, ya kuma cika wa'adinsa.
22 Amma Hannatu ba ta tafi ba, sai ta ce wa mijinta, “Da zarar an yaye yaron, zan kai shi domin ya zauna a gidan Ubangiji muddin ransa.”