5 Sa'an nan Saul ya zo birnin Amalekawa ya yi kwanto a cikin kwari.
6 Ya ce wa Keniyawa, “Ku tafi, ku rabu da Amalekawa, don kada in hallaka ku tare da su, gama kun yi wa dukan Isra'ilawa karamci lokacin da suka fito daga Masar.” Keniyawa kuwa suka fita daga cikin Amalekawa.
7 Saul ya ci Amalekawa, tun daga Hawila har zuwa Shur, da yake gabashin Masar,
8 ya kama Agag Sarkin Amalekawa da rai, ya hallaka mutane ƙaƙaf da takobi.
9 Amma Saul da jama'arsa suka bar Agag da rai, ba su kuma kashe tumaki da takarkarai mafi kyau ba, da 'yan maruƙa, da raguna, da dukan abin da yake mai kyau, bai yarda su hallaka su duka ba, amma sun hallaka dukan abin da yake rainanne ko marar amfani.
10-11 Sai Ubangiji ya yi magana da Sama'ila ya ce, “Na yi baƙin ciki da na sa Saul ya zama sarki, gama ya rabu da ni, ya yi rashin biyayya ga umarnaina,” Sama'ila kuwa ya yi fushi, ya yi ta roƙo ga Ubangiji dukan dare.
12 Sa'an nan ya tashi tun da sassafe domin ya sadu da Saul. Aka faɗa wa Sama'ila, Saul ya tafi Karmel, ya kafa wa kansa al'amudi, sa'an nan ya juya ya wuce zuwa Gilgal.