18 Sai wani daga cikin samarin ya amsa, ya ce, “Na san wani ɗan Yesse mutumin Baitalami. Shi gwanin kiɗan garaya ne, jarumi ne kuma, mayaƙi, mai lafazi, kyakkyawa, Ubangiji kuwa yana tare da shi.”
19 Sai Saul ya aiki manzanni zuwa wurin Yesse, ya ce, “Ka aiko mini da ɗanka, Dawuda, mai kiwon tumakinka.”
20 Yesse kuwa ya yi wa jaki labtu da abinci, da salkar ruwan inabi, da ɗan akuya, ya aiki Dawuda ɗansa, ya kai wa Saul.
21 Sa'an nan Dawuda ya zo wurin Saul, ya kama aiki. Saul kuwa ya ƙaunaci Dawuda ƙwarai, har Dawuda ya zama mai ɗaukar masa makamai.
22 Sa'an nan Saul ya aika wa Yesse cewa, “Ina so Dawuda. Ka bar shi ya zauna nan ya yi mini aiki.”
23 Tun daga ran nan zuwa gaba, a duk lokacin da mugun ruhun nan da Allah ya sa masa ya hau kansa, sai Dawuda ya ɗauki garaya, ya kaɗa masa. Sa'an nan mugun ruhun ya sauka, sai Saul ya wartsake.