3 Ka gayyaci Yesse zuwa wurin hadayar, zan nuna maka abin da za ka yi. Za ka zuba wa wanda na nuna maka mai.”
4 Sama'ila ya yi yadda Ubangiji ya faɗa masa, ya tafi Baitalami, inda dattawan garin suka tarye shi da rawar jiki, suka ce masa, “Maigani, wannan ziyara lafiya kuwa?”
5 Ya ce, “I, lafiya lau. Na zo ne in miƙa wa Ubangiji hadaya, sai ku tsarkake kanku, ku zo mu tafi wurin yin hadaya tare.” Ya kuma sa Yesse da 'ya'yansa maza su tsarkake kansu, su je wurin hadayar.
6 Da suka isa wurin hadayar, Sama'ila ya ga Eliyab, ɗan Yesse, sai ya zaci shi ne wanda Ubangiji ya zaɓa.
7 Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka kula da kyan tsarinsa, ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”
8 Sa'an nan Yesse ya kira Abinadab ya wuce a gaban Sama'ila. Amma Sama'ila ya ce, “Ubangiji kuma bai zaɓi wannan ba.”
9 Sa'an nan Yesse ya sa Shimeya ya zo. Sama'ila kuma ya ce, “Ubangiji bai zaɓi wannan ba.”