48 Goliyat kuwa ya fara gusowa ya gamu da Dawuda, sai Dawuda ya sheƙa zuwa bakin dāgar yaƙin don ya gamu da shi.
49 Sa'an nan Dawuda ya ɗauko dutse daga cikin angararsa, ya wurga, dutsen kuwa ya sami Goliyat a goshi, har ya lume. Goliyat kuwa ya faɗi rubda ciki.
50 Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara da Bafilisten. Ya buge shi, ya kashe shi ba tare da takobi a hannunsa ba.
51 Sa'an nan ya sheƙa zuwa wurin Bafilisten, ya zare takobin Bafilisten daga kubensa, ya datse masa kai da shi.Da Filistiyawa suka ga jaruminsu ya mutu, sai suka gudu.
52 Mutanen Isra'ila da na Yahuza suka tashi suka runtumi Filistiyawa, suna ihu, har zuwa Gat da ƙofofin Ekron. Filistiyawan da aka yi wa rauni suka yi ta faɗuwa a hanya tun daga Shayarim, har zuwa Gat da Ekron.
53 Da Isra'ilawa suka komo daga runtumar Filistiyawa, suka wāshe sansanin Filistiyawa.
54 Dawuda kuwa ya ɗauki kan Bafilisten ya kawo Urushalima, amma ya ajiye kayan yaƙin Bafilisten a alfarwarsa.