20 Sai ya aika da manzanni su tafi su kama Dawuda. Da suka kai, suka iske ƙungiyar annabawa suna annabci, Sama'ila kuwa yana tsaye a gabansu. Ruhun Allah ya sauko a kan manzannin Saul, su kuma suka yi annabci.
21 Aka faɗa wa Saul, sai ya sāke aiken waɗansu, su kuma suka shiga yin annabci. Ya kuma sāke aiken manzanni aji na uku, su kuma suka shiga yin annabci.
22 Saul kuma ya tafi Rama da kansa. Da ya kai babbar rijiyar da suke a Seku, sai ya tambayi inda Sama'ila da Dawuda suke. Wani ya ce masa, “Suna Nayot ta Rama.”
23 Sai ya tashi daga can zuwa Nayot ta Rama. Ruhun Allah kuwa ya sauko a kansa, sai shi kuma ya shiga yin annabci har ya kai Nayot ta Rama,
24 ya kuma tuɓe tufafinsa, ya yi ta annabci a gaban Sama'ila. Ya kwanta huntu dukan yini da dukan dare. Don haka aka riƙa yin karin magana da cewa, “Har Saul ma yana cikin annabawa?”