4 Jonatan kuwa ya yabi Dawuda a gaban Saul, ya ce masa, “Kada sarki ya yi wa baransa, Dawuda, laifi, gama shi bai yi maka laifi ba, ayyukansa kuma a gare ka masu kyau ne.
5 Ya yi kasai da ransa har ya kashe Bafilisten, Ubangiji kuwa ya ba Isra'ilawa babbar nasara. Kai ma ka gani, ka kuwa yi murna. Me ya sa za ka ɗauki alhakin Dawuda, wanda bai yi maka laifin kome ba?”
6 Saul kuwa ya saurari maganar Jonatan, ya rantse masa ya ce, “Hakika, ba za a kashe shi ba.”
7 Jonatan kuwa ya kira Dawuda ya faɗa masa dukan abin da Saul ya faɗa. Ya kuma kai Dawuda gaban Saul, ya zauna tare da shi kamar dā.
8 Aka kuma yi yaƙi da Filistiyawa, Dawuda kuwa ya tafi ya yi yaƙi da su, ya kashe su da yawa, sai suka gudu a gabansa.
9 Ubangiji kuma ya sa mugun ruhu ya sauko kan Saul sa'ad da yake zaune a gidansa, da mashi a hannunsa. Dawuda kuma yana ta kaɗa masa garaya.
10 Saul kuwa ya yi shiri ya nashi Dawuda, ya kafe shi ga bango. Da ya nashe shi, sai ya goce, mashin ya sami bangon. Dawuda kuwa ya gudu, ya tsere.