8 Yakan tā da matalauci daga cikin ƙura,Yakan ɗaga mai bukata daga zaman baƙin ciki.Ya sa su zama abokan 'ya'yan sarki,Ya ɗora su a wurare masu maƙami.Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne,A kansu ya kafa duniya.
9 “Zai kiyaye rayukan amintattunmutanensa,Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu,Ba ƙarfin mutum yake sa ya yi nasara ba.
10 Za a hallakar da maƙiyan Ubangiji,Zai yi musu tsawa daga Sama.Ubangiji zai hukunta dukan duniya,Zai ba sarkinsa iko,Zai sa zaɓaɓɓen sarkinsa ya zamamai nasara.”
11 Sa'an nan Elkana ya koma gidansa a Rama, amma yaron ya zauna a Shilo, yana aikin Ubangiji a hannun Eli, firist.
12 'Ya'yan Eli, maza kuwa, ba su da kirki, ba su kula da Ubangiji ba,
13 Ko ka'idodi game da abin da firistoci za su karɓa a hannun jama'a. A maimakon haka, lokacin da mutum ya je domin ya miƙa hadayarsa, sai baran firist ya zo da rino a hannunsa a sa'ad da ake dafa naman.
14 Sai ya caka rinon a cikin tukunyar, to, duk abin da ya cako wannan ya zama na firist. Haka suka yi ta yi wa dukan Isra'ilawa da suka zo miƙa hadaya a Shilo.