23 Ku lura sosai da dukan wuraren da yake ɓuya, sa'an nan ku komo mini da tabbataccen labari. Sa'an nan zan tafi tare da ku. Idan yana ƙasar, zan neme shi ko'ina a ƙasar Yahuza.”
24 Sai suka yi gaba, suka tafi Zif. Dawuda da mutanensa kuwa suna jejin Mawon, cikin Araba, kudu da Yeshimon.
25 Saul da mutanensa suka tafi neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya sauka daga dutsen ya zauna a can jejin Mawon. Da Saul ya ji, sai ya bi Dawuda zuwa jejin Mawon.
26 Saul yana gefe ɗaya na dutsen, Dawuda kuma da mutanensa suna wancan gefe. Dawuda ya yi sauri ya tsere daga Saul domin Saul da mutanensa suna ƙoƙari su kewaye su, su kama su.
27 Suna bin su Dawuda kusa kusa, sai manzo ya zo ya ce wa Saul, “Sai ka komo da sauri domin Filistiyawa sun kawo wa ƙasar hari.”
28 Saul kuwa ya koma daga bin Dawuda, ya tafi, ya yi yaƙi da Filistiyawa, domin haka aka riƙa kiran wurin, Sela-hammalekot, wato dutsen tserewa.
29 Dawuda kuwa ya tashi daga can, ya tafi jejin En-gedi inda ya ɓuya.