12 Ubangiji dai zai shara'anta tsakanina da kai, ya sāke mini, amma hannuna ba zai taɓa ka ba.
13 Mutanen dā suna da karin magana cewa, ‘Daga cikin masu mugunta mugunta take fitowa.’ Hannuna dai ba zai taɓa ka ba.
14 Shin, sawun wa Sarkin Isra'ila yake bi? Wane ne kuma kake runtuma? Kana bin sawun mataccen kare, da sawun tunkuyau?
15 Ubangiji ne zai zama alƙali, ya hukunta tsakanina da kai. Zai tsaya mini, ya cece ni daga hannunka.”
16 Da Dawuda ya gama faɗa wa Saul wannan magana, sai Saul ya ce, “Ɗana, Dawuda, muryarka ke nan?” Ya yi kuka da ƙarfi.
17 Sa'an nan ya ce wa Dawuda, “Ka fi ni adalci, gama ka yi mini alheri, ni kuwa na yi maka mugunta.
18 Yau ka nuna a sarari yadda ka yi mini alheri. Ubangiji ya bashe ni a hannunka, amma ba ka kashe ni ba.