17 Saul ya gane da muryar Dawuda, ya ce, “Muryarka ke nan ɗana, Dawuda?”Dawuda ya amsa, “I, muryata ce, ya mai girma sarki.”
18 Sai ya ƙara da cewa, “Me ya sa mai girma yake bin sawun baransa? Me na yi? Mene ne laifina?
19 Bari sarki ya kasa kunne ga maganar baransa. Idan Ubangiji ne ya kuta ka ka yi gāba da ni, to, bari ya karɓi hadaya, amma idan mutane ne, to, bari su zama la'anannu, gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Tafi ka bauta wa alloli.’
20 Kada ka kashe ni a baƙuwar ƙasa nesa da Ubangiji. Don me Sarkin Isra'ila yake so ya kashe ni, ni da nake kamar tunkuyau? Don me zai farauce ni kamar tsuntsun jeji?”
21 Sa'an nan Saul ya ce, “Na yi laifi, ka komo, ɗana Dawuda, ba zan yi maka kome ba, gama raina ya zama da daraja a gare ka kyau. Na yi aikin wauta, na yi laifi da yawa.”
22 Sai Dawuda ya ce, “Ga mashinka! Ka aiko wani saurayi ya zo ya karɓa.
23 Ubangiji dai zai sāka wa kowa bisa ga adalcinsa da amincinsa. Ubangiji ya bashe ka a hannuna yau, amma na ƙi in kashe wanda Ubangiji ya keɓe.