7 Sai ya ce wa barorinsa, “Ku nemo mini wata mace mai duba domin in tafi wurinta in yi tambaya.”Barorinsa suka ce masa, “Ai, akwai wata mai duba a Endor.”
8 Sai Saul ya ɓad da kama, ya sa waɗansu tufafi. Shi da waɗansu mutum biyu suka tafi wurin matar da dare. Ya ce mata, “Ina roƙonki ki duba mini ta hanyar sihiri. Ki hawar mini da duk wanda zan faɗa miki.”
9 Matar ta ce masa, “Hakika ka san abin da sarki Saul ya yi, yadda ya karkashe masu duba da masu maita a ƙasar. Me ya sa kake ƙoƙarin kafa mini tarko, don ka sa a kashe ni?”
10 Saul ya rantse mata da Ubangiji, ya ce, “Hakika, ba za a hukunta ki saboda wannan ba.”
11 Sai matar ta ce, “Wa kake so in hawar maka?”Ya ce, “Ki hawar mini da Sama'ila.”
12 Da matar ta ga Sama'ila, sai ta fasa ƙara, ta ce wa Saul, “Don me ka ruɗe ni, ashe, kai ne sarki Saul?”
13 Sarki kuwa ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, me kike gani?”Ta ce masa, “Na ga wani allah yana fitowa daga ƙasa.”