8 Sai Saul ya ɓad da kama, ya sa waɗansu tufafi. Shi da waɗansu mutum biyu suka tafi wurin matar da dare. Ya ce mata, “Ina roƙonki ki duba mini ta hanyar sihiri. Ki hawar mini da duk wanda zan faɗa miki.”
9 Matar ta ce masa, “Hakika ka san abin da sarki Saul ya yi, yadda ya karkashe masu duba da masu maita a ƙasar. Me ya sa kake ƙoƙarin kafa mini tarko, don ka sa a kashe ni?”
10 Saul ya rantse mata da Ubangiji, ya ce, “Hakika, ba za a hukunta ki saboda wannan ba.”
11 Sai matar ta ce, “Wa kake so in hawar maka?”Ya ce, “Ki hawar mini da Sama'ila.”
12 Da matar ta ga Sama'ila, sai ta fasa ƙara, ta ce wa Saul, “Don me ka ruɗe ni, ashe, kai ne sarki Saul?”
13 Sarki kuwa ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, me kike gani?”Ta ce masa, “Na ga wani allah yana fitowa daga ƙasa.”
14 Ya ce mata, “Yaya kamanninsa yake?”Ta ce, “Wani tsoho ne yake hawowa, yana naɗe da alkyabba.”Saul ya gane Sama'ila ne, sai ya sunkuyar da kai, ya durƙusa har ƙasa da bangirma.