2 Filistiyawa suka ci Saul da 'ya'yansa maza. Suka kashe Jonatan, da Abinadab, da Malkishuwa, 'ya'yan Saul.
3 Yaƙin ya matsa wa Saul. Maharba suka harbe shi, suka yi masa mummunan rauni.
4 Sai ya ce wa mai ɗaukar masa makamai, “Ka zare takobinka ka sha zarata da shi domin kada marasa kaciyan nan su zo su sha zarata, su yi mini ba'a.” Amma mai ɗaukar masa makamai bai yarda ba, domin ya ji tsoro da yawa. Sai Saul ya zare takobinsa, ya faɗa a kansa.
5 Da mai ɗaukar masa makamai ya ga Saul ya rasu, shi ma ya fāɗa a kan nasa takobi ya mutu tare da Saul.
6 Haka Saul, da 'ya'yansa maza guda uku, da mai ɗaukar masa makamai, da dukan mutanen da suke tare da shi suka mutu a rana ɗaya.
7 Sa'ad da Isra'ilawan da suke a wancan hayi na kwarin da waɗanda suke a wancan hayin Urdun suka ga mayaƙan Isra'ila sun gudu, Saul kuma da 'ya'yansa sun mutu, sai suka bar garuruwansu, suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu.
8 Da Filistiyawa suka zo kashegari don su washe kayan kisassun, sai suka tarar da gawar Saul da gawawwakin 'ya'yansa uku a kan Dutsen Gilbowa.