10 Sa'an nan Sarauniyar Sheba ta ba sarki talanti ɗari da ashirin na zinariya,da kayan yaji mai yawan gaske, da duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kawo kayan yaji da yawa kamar yadda Sarauniyar Sheba ta kawo wa sarki Sulemanu ba.
11 Bayan wannan kuma jiragen ruwa na Hiram da suka kawo zinariya daga Ofir, sun kuma kawo itacen almug da yawa, da duwatsu masu daraja daga can.
12 Da itacen almug ne sarki ya yi ginshiƙai na Haikalin Ubangiji da gidan sarki, ya kuma yi molaye da garayu domin mawaƙa. Har wa yau ba a taɓa samu, ko ganin irin itacen almug kamar wannan ba.
13 Sarki Sulemanu ya ba Sarauniyar Sheba duk abin da ta nuna tana bukata, banda kyautar karamcin da ya yi mata. Sai ta koma ƙasarta tare da barorinta.
14 Yawan zinariya da akan kawo wa Sulemanu kowace shekara yakan kai talanti ɗari shida da sittin da shida na zinariya.
15 Banda wanda ya sa wa 'yan kasuwa, da fatake, da harajin dukan sarakunan Arabiya, da na hakimai.
16 Sarki Sulemanu ya yi manyan garkuwoyi guda ɗari biyu da zinariya. Anyi kowace garkuwa da shekel ɗari shida na zinariya.