4 A lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji, Obadiya ya kwashe annabawa ɗari ya raba su hamsin hamsin ya ɓoye su a kogo, ya ciyar da su, ya shayar da su.
5 Sai Ahab ya ce wa Obadiya, “Ka tafi ko'ina a ƙasar duk inda maɓuɓɓugan ruwa suke, da inda fadamu suke duka, watakila ma sami ciyawa mu ceci rayukan dawakai da alfadarai, don kada mu rasa waɗansu.”
6 Saboda haka suka rabu biyu don su zagaya. Ahab ya bi waje guda, shi kuma ya bi ɗaya wajen.
7 Sa'ad da Obadiya yake tafiya a hanya suka yi kaciɓis da Iliya, Obadiya kuwa ya rabe da shi, sai ya rusuna ya ce, “Shugabana Iliya, kai ne kuwa?”
8 Iliya ya amsa masa ya ce, “Ni ne. Tafi, ka faɗa wa shugabanka, sarki, cewa ga ni nan.”
9 Obadiya ya ce, “Wane laifi na yi, har da za ka ba da ni a hannun Ahab ya kashe ni?
10 Na rantse da Ubangiji Allahnka mai rai, ba al'umma ko mulki da shugabana sarki bai aika a nemo ka ba. In suka ce ba ka nan, sai ya sa mulkin ko al'ummar su rantse, cewa ai, ba su same ka ba.