28 Yadda aka yi dakalan ke nan, dakalan suna da sassa, sassan kuma suna da mahaɗai.
29 Aka zana hotunan zakoki, da na bijimai, da na kerubobi a kan sassan. A kan mahaɗan kuma akwai gammo, aka zana hotunan furanni a ƙarƙashin zakokin da bijiman.
30 Kowane dakali yana da ƙafa huɗu na tagulla kamar na karusa, da sandunan tagulla don sa kwatarniya. A kusurwoyin akwai abubuwa na zubi don tallabar kwatarniya. An zana furanni a kowane gefensu.
31 Bakinsa daga cikin dajiyar ya yi sama kamu guda. Bakin da'ira ne kamar fasalin gammo, kamu ɗaya da rabi. Akwai zāne-zāne a bakin. Sassan murabba'i ne, ba da'ira ba.
32 Ƙafafu huɗu ɗin, suna ƙarƙashin sassan. Sandunan ƙafafun a haɗe suke da dakalan. Tsayin kowace ƙafa kuwa kamu ɗaya da rabi ne.
33 Ƙafafun suna kama da ƙafafun karusa. Sandunan ƙafafun, da gyaffansu, da kome na ƙafafun duka na zubi ne.
34 Akwai ginshiƙi huɗu daga ƙarƙashin kowane dakali. Ginshiƙan suna haɗe da dakalan.