21 A cikin Haikalin kuma na shirya wa akwatin alkawari wuri, inda alkawarin Ubangiji yake, wato alkawarin da ya yi wa kakanninmu sa'ad da ya fito da su daga ƙasar Masar.”
22 Sa'an nan Sulemanu ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji a gaban dukan taron jama'ar Isra'ila. Ya ɗaga hannuwansa sama,
23 ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ba wani Allah kamarka cikin Sama a bisa, da cikin duniya a ƙasa, wanda yake cika alkawari, ya nuna ƙauna ga bayinsa, waɗanda suke tafiya a gabansa da zuciya ɗaya.
24 Kai wanda ka cika abin da ka faɗa wa bawanka, Dawuda, tsohona, i, abin da ka faɗa da bakinka ka cika shi yau.
25 Yanzu fa, ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ka cika wa bawanka Dawuda, tsohona, sauran abin da ka alkawarta masa, da ka ce, ‘Ba za ka rasa mutum a gabana wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba, in dai zuriyarka sun mai da hankali, sun yi tafiya a gabana kamar yadda kai ka yi.’
26 Yanzu fa, ya Allah na Isra'ila, sai ka tabbatar da maganarka wadda ka yi wa bawanka, Dawuda, tsohona.
27 “Amma ko Allah zai zauna a duniya? Ga shi, Saman sammai ba ta isa ta karɓe ka ba, balle wannan Haikali da na gina!