31 “Idan mutum ya yi wa maƙwabcinsa laifi, aka ba shi rantsuwa, idan ya zo, ya rantse a gaban bagadenka a wannan Haikali,
32 ya Ubangiji ka ji daga Sama, ka shara'anta bayinka, ka hukunta mai laifin, ka ɗora masa hakkinsa a kansa, amma ka kuɓutar da mara laifin, ka sāka masa bisa ga adalcinsa.
33 “Lokacin da abokan gāba suka ci mutanenka Isra'ila da yaƙi, saboda sun yi maka zunubi, idan sun komo wurinka, suka yabe ka, suka yi addu'a, suka roƙe ka a wannan Haikali,
34 sai ka ji daga Sama, ka gafarta wa jama'ar Isra'ila zunubinsu, sa'an nan ka sāke komar da su zuwa ƙasar da ka ba kakanninsu.
35 “Idan an hore su da rashin ruwan sama, saboda sun yi maka zunubi, idan sun tuba, suna fuskantar wannan Haikali, suka yi addu'a, suka kuma yabe ka,
36 sai ka ji daga Sama, ka gafarta zunuban sarki, da na jama'arka Isra'ila. Ka koya musu kyakkyawar hanyar da za su bi, ka sa a yi ruwan sama a ƙasarka wadda ka ba jama'arka gādo.
37 “Idan akwai yunwa a ƙasar, ko kuma akwai annoba, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fāri, ko tsutsa, sun cinye amfanin gona, idan kuma abokan gāba sun kawo wa jama'arka yaƙi har ƙofar birninsu, duk dai irin annoba da ciwon da yake cikinsu,