22 Bakan Jonatan mai kisa ne,Takobin Saul ba shi da jinƙai,Yana kashe masu iko, yana kuma kashe abokan gāba.
23 “Saul da Jonatan ƙaunatattu ne, suna da bansha'awa,A raye suna tare, haka kuma a mace suna tare.Sun fi gaggafa sauri,Sun fi zaki ƙarfi.
24 “Ku 'yan matan Isra'ila, ku yi makoki domin Saul!Ya suturta ku da mulufi mai ƙayatarwa,Ya yi muku adon lu'ulu'u da zinariya.
25 “Jarumawa sun fāɗi,An kashe su a bakin dāga.Jonatan na kwance matacce a tuddai.
26 “Na damu ƙwarai saboda kai, ɗan'uwana Jonatan,Ƙaunatacce kake a gare ni!Ƙaunarka a gare ni abar al'ajabi ce,Ta fi ƙaunar mace.
27 “Jarumawa sun fāɗi,Makamansu ba su da sauran amfani.”