18 Sai sarki ya ce mata, “Kada ki rufe mini duk abin da zan tambaye ki.”Ta ce, “To, ka yi tambayarka.”
19 Sa'an nan ya ce mata, “Ko akwai hannun Yowab cikin dukan sha'anin nan naki?”Ita kuwa ta amsa, “Na rantse da kai, ya ubangijina, sarki, ba dama a yi maka ƙumbiya-ƙumbiya. Haka ne, Yowab baranka ne ya sa ni. Shi ya sa dukan waɗannan magana a bakin baranyarka.
20 Yowab baranka ya yi wannan don ya daidaita al'amarin. Amma ubangijina yana da hikima irin ta mala'ikan Allah domin ya san dukan al'amuran da suke a duniya.”
21 Sa'an nan sarki ya ce wa Yowab, “To, na yarda, sai ka tafi ka komo da saurayin nan, Absalom.”
22 Sai Yowab ya rusuna har ƙasa da bangirma, ya yi wa sarki kyakkyawan fata. Ya kuma ce, “Yau na sani na sami tagomashi a wurinka, ya ubangijina, sarki, da yake ka amsa roƙona.”
23 Sa'an nan Yowab ya tashi, ya tafi Geshur, ya komo da Absalom Urushalima.
24 Sarki ya ce a sa shi ya koma gidansa, kada ya zo gabansa. Absalom kuwa ya yi zamansa can gidansa, bai je gaban sarki ba.