22 Sai Yowab ya rusuna har ƙasa da bangirma, ya yi wa sarki kyakkyawan fata. Ya kuma ce, “Yau na sani na sami tagomashi a wurinka, ya ubangijina, sarki, da yake ka amsa roƙona.”
23 Sa'an nan Yowab ya tashi, ya tafi Geshur, ya komo da Absalom Urushalima.
24 Sarki ya ce a sa shi ya koma gidansa, kada ya zo gabansa. Absalom kuwa ya yi zamansa can gidansa, bai je gaban sarki ba.
25 A cikin Isra'ila duka ba wanda ake yaba kyansa kamar Absalom. Tun daga tafin sawunsa har zuwa bisa kansa ba shi da makusa.
26 Sa'ad da ya yi aski yakan auna nauyin gashin kansa, nauyin yakan kai wajen shekel ɗari biyu. Gama a ƙarshen kowace shekara yake aski, sa'ad da gashin ya yi masa nauyi.
27 Aka haifa wa Absalom 'ya'ya uku maza da 'ya mace guda, sunanta Tamar, ita kuwa kyakkyawa ce.
28 Absalom ya yi shekara biyu cif a Urushalima, amma bai sami izinin ganin sarki ba.