18 Amma wani saurayi ya gan su, sai ya faɗa wa Absalom. Sai su biyu ɗin suka gudu nan da nan. Suka shiga gidan wani mutum a Bahurim, akwai rijiya a filin gidan. Sai suka shiga rijiyar.
19 Matar gidan kuwa ta yi shimfiɗa a bakin rijiyar, ta baza tsaba a kai, ba kuwa wanda ya san abin da ta yi.
20 Sa'ad da fādawan Absalom suka zo gidan, suka tambayi matar, “Ina Ahimawaz da Jonatan suke?”Sai ta ce musu, “Ai, tuni sun haye kogi.”Sa'ad da suka neme su ba su same su ba, sai suka koma Urushalima.
21 Bayan da fādawan sun tafi, sai mutanen suka fito daga rijiyar. Suka tafi suka ce wa sarki Dawuda, “Ka tashi ka haye kogin nan da nan, gama ka ji irin muguwar shawarar da Ahitofel ya bayar a kanka.”
22 Sai Dawuda da dukan mutanen da suke tare da shi suka haye Urdun. Kafin wayewar gari ko wannensu ya haye Urdun.
23 Da Ahitofel ya ga ba a bi shawararsa ba, sai ya yi wa jakinsa shimfiɗa ya hau, ya koma garinsu. Da ya kintsa gidansa, sai ya rataye kansa, ya mutu, aka binne shi a kabarin mahaifinsa.
24 Dawuda kuwa ya zo Mahanayim. Absalom kuma da dukan mutanen Isra'ila suka haye Urdun.