12 Ya ce, “Ai, ku 'yan'uwana ne, da ƙasusuwana, da namana. To, me ya sa za ku zama na ƙarshe a kan komar da sarki?
13 Ku ce wa Amasa, ‘Ashe, kai ba ƙashina da namana ba ne? Allah ya hukunta ni idan ba kai ne shugaban rundunar sojojina a maimakon Yowab ba.’ ”
14 Da haka Dawuda ya rinjayi zukatan mutanen Yahuza, suka zama ɗaya, kamar mutum guda. Sai suka aika wurin sarki, cewa, ya komo tare da dukan fādawansa.
15 Sa'ad da sarki ya iso Urdun. Mutanen Yahuza suka tafi Gilgal suka taryi sarki, domin su hawo da shi Urdun.
16 Shimai ɗan Gera kuma, mutumin Biliyaminu daga Bahurim, ya gaggauta, ya gangara tare da mutanen Yahuza don ya taryi sarki Dawuda.
17 Ya zo tare da mutum dubu (1,000) daga kabilar Biliyaminu. Ziba kuma, baran gidan Saul, ya zo a gaggauce a gaban sarki a Urdun tare da 'ya'yansa maza, su goma sha biyar, da barorinsa guda ashirin.
18 Suka haye zuwa wancan hayi don su hawo da iyalin sarki, su kuma yi masa abin da zai ji daɗi.Sa'ad da sarki yake shirin hayewa, sai Shimai ɗan Gera ya zo ya fāɗi a gābansa.