18 'Ya'yan Zeruya, maza, su uku suna nan, wato Yowab, da Abishai, da Asahel. Asahel maguji ne kamar barewa.
19 Sai ya tasar wa bin Abner haiƙan, bai kauce ba.
20 Da Abner ya waiga, sai ya ce, “Kai ne Asahel?”Ya amsa, “Ni ne.”
21 Abner ya ce masa, “Ka daina haye mini, ka runtumi ɗaya daga cikin samarin, ka kama shi, ka karɓe masa makaminsa.” Amma Asahel bai daina binsa ba.
22 Abner kuma ya sāke ce masa, “Ka daina bina, kada ka sa in kashe ka fa! Idan na kashe ka kuwa, yaya zan yi ido biyu da dan'uwanka, Yowab?”
23 Amma Asahel bai daina binsa ba, Abner dai ya nashe shi da gindin māshi a ciki, sai mashin ya fita ta bayansa. Ya fāɗi ya mutu nan take. Duk wanda ya zo inda Asahel ya fāɗi ya mutu, sai ya tsaya cik.
24 Amma Yowab da Abishai suka bi Abner, har faɗuwar rana, suka isa tudun Amma, wanda yake gaban Gaiya, a hanya zuwa jejin Gibeyon.