7 A cikin kai da kawowata tare da dukan jama'ar Isra'ila ban taɓa ce wa wani daga cikin shugabannin Isra'ila waɗanda na sa su lura da jama'ata Isra'ila, ya gina mini ɗaki na katakon al'ul ba.’
8 Abin da za ka faɗa wa bawana Dawuda ke nan, in ji Ubangiji Mai Runduna, ‘Na ɗauko ka daga makiyaya inda kake kiwon tumaki domin ka zama sarkin jama'ata Isra'ila.
9 Ban kuwa rabu da kai ba duk inda ka tafi, na kuma kawar da abokan gābanka duka. Zan sa ka shahara kamar shahararrun mutane na duniya.
10-11 Zan nuna wa jama'ata Isra'ila wuri na kansu inda zan kafa su su zauna. Ba wanda zai sāke damunsu. Mugayen mutane kuma ba za su ƙara wahalshe su kamar dā ba, tun lokacin da na naɗa wa jama'ata Isra'ila mahukunta. Zan hutar da kai daga fitinar abokan gābanka duka. Banda wannan kuma ina shaida maka, cewa, zan sa gidanka ya kahu.
12 Sa'ad da kwanakinka suka ƙare, za ka rasu tare da kakanninka. A bayanka, zan ta da ɗanka, na cikinka. Zan sa mulkinsa ya kahu.
13 Shi ne zai gina mini ɗaki. Ni kuwa zan tabbatar da kursiyin sarautarsa har abada.
14 Zan zama uba gare shi, zai kuma zama ɗa a gare ni. Sa'ad da ya yi laifi zan hukunta shi da sanda kamar yadda mutane suke yi. Zan yi masa bulala kamar yadda 'yan adam suke yi.