9 Ban kuwa rabu da kai ba duk inda ka tafi, na kuma kawar da abokan gābanka duka. Zan sa ka shahara kamar shahararrun mutane na duniya.
10-11 Zan nuna wa jama'ata Isra'ila wuri na kansu inda zan kafa su su zauna. Ba wanda zai sāke damunsu. Mugayen mutane kuma ba za su ƙara wahalshe su kamar dā ba, tun lokacin da na naɗa wa jama'ata Isra'ila mahukunta. Zan hutar da kai daga fitinar abokan gābanka duka. Banda wannan kuma ina shaida maka, cewa, zan sa gidanka ya kahu.
12 Sa'ad da kwanakinka suka ƙare, za ka rasu tare da kakanninka. A bayanka, zan ta da ɗanka, na cikinka. Zan sa mulkinsa ya kahu.
13 Shi ne zai gina mini ɗaki. Ni kuwa zan tabbatar da kursiyin sarautarsa har abada.
14 Zan zama uba gare shi, zai kuma zama ɗa a gare ni. Sa'ad da ya yi laifi zan hukunta shi da sanda kamar yadda mutane suke yi. Zan yi masa bulala kamar yadda 'yan adam suke yi.
15 Amma ba zan daina nuna masa madawwamiyar ƙaunata ba, kamar yadda na yi wa Saul wanda na kawar daga fuskata.
16 Gidanka kuwa da mulkinka za su dawwama a gabana har abada. Gadon sarautarka kuma zai kahu har abada.’ ”